Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Sama Da 20 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Sama Da 20 A Zamfara

33
0

‘Yan bindiga sun kashe sama da manoma 20 a yankin Gidan
Goga da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya tabbatar wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kai wa manoman hari ne bayan sun shagaltu da aikin noma, inda su ka yi yunƙurin yin garkuwa da wasu daga cikin su.

Ya ce Maharan sun afka wa manoman ne a ƙoƙarin su na yin garkuwa da wasu, amma sun fahimci cewa manoman sun fara gudun neman tsira, don haka sai su ka fara harbin su ɗaya bayan ɗaya, ya na mai bada tabbacin cewa yanzu haka akwai gawarwakin mutane 22 da aka kashe.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce mutane tara ne su ka mutu, yayin da biyar su ka jikkata kuma a halin yanzu ana kula da lafiyar su.

Leave a Reply