Home Labarai Apc Ta Roƙi Kotu Ta Kori Ƙararrakin Da Jam’Iyyu Uku Su Ka...

Apc Ta Roƙi Kotu Ta Kori Ƙararrakin Da Jam’Iyyu Uku Su Ka Shigar

85
0

Jam’iyyar APC, ta roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da
ƙararrakin da jam’iyyun AA da APM da APP su ka shigar
domin kalubalantar nasarar Bola Tinubu.

APC ta roƙi Kotun Shari’ar Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa na shekara ta 2023 cewa ta kori dukkan ƙararrakin uku da jam’iyyun su ka shigar daban-daban.

Lauyan APC Thomas Ojo ne ya shigar da ƙarar, wanda ya na daga cikin lauyoyin da ke kare jam’iyyar a ƙarƙashin babban lauya Lateef Fagbemi a Abuja.

Tuni dai jam’iyyar APP ta bi sahun sauran jam’iyyun, inda ta garzaya kotu domin jayayya da nasarar da Bola Tinubu da APC su ka yi a zaɓen shugaban ƙasa.

Leave a Reply