Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 2, Sun Sace Dan Kasuwa a Kano

‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 2, Sun Sace Dan Kasuwa a Kano

1
0

Akalla mutane biyu ‘yan bindiga su ka harbe, tare da yin
awon gaba da wani dan kasuwa mai suna Nasiru Na’ayya a
kauyen Gangarbi da ke Karamar Hukumar Rogo ta Jihar
Kano.

Wani ganau kuma dan’uwa ga dan kasuwar da aka sace, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari gidan Na’ayya ne da misalin karfe 12 na dare su na ta harbe-harbe.

Ya ce da mutanen yankin su ka yi yunkurin hana ‘yan bindigar sace shi ne su ka aharbe mutane biyu, lamarin da ya kai ga mutuwar daya nan take, wani kuma ya samu raunin da a halin yanzu ya na jinya a asibiti.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta, ta ce a baya-bayan nan ne aka kai hare-hare a Gangarbi da kauyukan da ke makwaftaka da su kamar Bari da Gwangwan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano SP Abdullahi Kiyawa, ya ce ba ya da masaniyar faruwar lamarin, amma da zarar ya samu cikakken bayani zai sanar.