
Wani harin Bom da ake zargin Sojojin Nijeriya sun kai, ya yi sanadiyyar mutuwar Fulani makiyaya akalla 39, yayin da wasu da dama su ka samu raunuka a wani kauye da ke jihar Nasarawa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa Maiyaki Muhammad Baba, ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Rukubi da ke daf da iyakar jihar da makwafciyar ta jihar Benue, inda aka kirga gawarwakin makiyaya 27 da kuma dabbobi masu tarin yawa, ko da ya ke kungiyar Miyetti Allah MACBAN ta ce adadin ya kai mutane 39.
Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito kungiyar da ke kare hakkin makiyaya ta Miyetti Allah ta na cewa, jirgin Sojojin saman Nijeriya ne ya kaddamar da harin a kan makiyaya, lamarin da har zuwa yanzu Sojojin ba su musanta ba ko kuma bada bahasi a kan dalilin farmakin.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ta Muhammad Nura, kungiyar ta bukaci Sojojin su bada bahasi a kan kisan Makiyayan, wadanda ke kan hanyar su ta komawa daga biyan tarar Naira miliyan 29 da jihar Benue ta sanya masu bayan sun karya dokar kiwo.
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya sha alwashin gudanar da binciken a kan lamarin.
You must log in to post a comment.