Kotun sauraren shari’ar zabe a Nijeriya, ta yanke hukuncin soke zaben gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP, inda ta bayyana tsohon gwamna Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a shekarar da ta gabata.
Shugaban kwamitin alkalan da su ka saurari karar Terste Kume ya karanta hukuncin kotun a birnin Oshogbo, inda ya umurci hukumar zabe ta karbe takardar samun nasarar zaben da aka ba Adeleke a mika wa Oyetola.
Mai shari’a Kume, ya ce sun gamsu cewa hukumar zabe ta gudanar da zaben kamar yadda dokar zabe ta tanada, sai dai an samu kuri’un da su ka wuce kima a wasu mazabu, lamarin da ya sa aka janye alkaluman da ake tababa a kai.
Ya ce bayan janye wadancan haramtattun kuri’un, sakamakon zaben ya nuna cewa Oyetola ya lashe zaben da aka yi da kuri’u dubu 314 da 921, don haka ta bada umurnin a rantsar da shi a matsayin wanda ya samu nasara.
Sai dai Adeleke ya ce zai ɗauka ƙara game da hukuncin da kotun ta yanke, inda ta soke zaɓen da aka yi masa a matsayin gwamnan jihar Osun.
You must log in to post a comment.