Home Labaru Ilimi Ana Gallaza Wa Ɗalibai Musulmai A Jami’o’i Mallakin Kiristoci A Nijeriya –...

Ana Gallaza Wa Ɗalibai Musulmai A Jami’o’i Mallakin Kiristoci A Nijeriya – MURIC

84
0

Ƙungiyar Kare Muradun Musulmai a Nijeriya MURIC, ta yi
zargin cewa ana gallaza wa ɗalibai Musulmi da ke karatu a
jami’o’i musu zaman kan su mallakin Kiristoci a Nijeriya

MURIC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa Shugaban ta Farfesa Ishaq Akintola ya sanya wa hannu.

A cikin sanarwar, kungiyar ta zargi jami’o’in da nuna gaba da tsana da kuma tsangwama ga Musulmi da kuma adddinin Musulunci, ta yadda ake tursasa dalibai Musulmai zuwa Coci da a kuma hana su sanya hijabi da sauran su.

Farfesa Ishaq Akintola, ya ce sun samu rahotanni da yawa a kan yadda jami’oin masu zaman kansu mallakin Kiristoci ke nuna wa ɗalibai Musulmai kyama da wariya, ta yadda ba su iya yin addinin su yadda ya kamata.

Shugaban kungiyar, ya ce hakan take haƙƙin ɗalibai Musulmi ne da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba su, sannan ya yi kira ga hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa ta gaggauta tsaftace waɗannan jami’o’i.

Leave a Reply