Home Home 1ST Class: Majalisa Ta Tattauna Kan Daukar Masu Digiri Aiki Kai Tsaye

1ST Class: Majalisa Ta Tattauna Kan Daukar Masu Digiri Aiki Kai Tsaye

65
0
Majalisar wakilai na son a fara daukar daliban da su ka kammala digiri da sakamako mafi kyau daga cibiyoyin ilimi na Nijeriya aiki kai tsaye.

Majalisar wakilai na son a fara daukar daliban da su ka kammala digiri da sakamako mafi kyau daga cibiyoyin ilimi na Nijeriya aiki kai tsaye.

Ta ce hakan zai zama hanyar karfafa kwarin gwiwa ga daliban Nijeriya, da kuma ba wadanda su ka kammala karatu damar kara kaimi a karatun su.

Dan majalisar wakilai da ya gabatar da kudirin Chinedu Martins, ya ce hakan zai magance matsalolin ficewar daliban Nijeriya masu hazaka zuwa kasashen ketare.

Chinedu Martins ya kuma jaddada cewa, jami’o’in Nijeriya su na samar da daruruwan daliban da su ka kammala karatun digiri da sakamako matakin farko a duk shekara, kuma Kashi mai yawa daga cikin su ya na da wahala su samu ayyukan yi da bada gudummawa wajen gina kasa.

Dan majalisar ya kuma koka da cewa, rashin samun abin yi a Nijeriya ya sa da yawa daga cikin hazikan daliban ke tsallakawa kasashen ketare domin samun madogara.