‘Yan majalisar dattawa na jam’iyyar APC sun tabbatar wa Bola Ahmed Tinubu cewa su na goyon bayan ya gaji shugaba Buhari a shekara ta 2023.
Tinubu dai ya kai ziyara majalisar dattawa domin neman goyon bayan ‘yan majalisu a kudurin sa na takarar shugaban ƙasa, inda ya gana da Sanatocin jam’iyyar APC a wani ɓangare na neman samun tikicin takara.
Yayin zaman kuwa, Tinubu ya roki ‘yan majalisun APC su taimaka ya samu tikitin takarar da zai ba shi damar fafatawa a zaben shugaban ƙasa na shekara ta 2023.
Ya ce ya kai kan shi Majalisar dattawa ne don neman alfarmar yin aiki tare, da kuma goyon bayan su wajen cika burin sa na zama shugaban ƙasa.
Da ya ke jawabin sa, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce dukkan su su na yi wa Tinubu fatan alkairi, tare da ba shi tabbacin cewa su na tare da shi.