Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekiti Jide Awe, ya ce mutanen Kudu maso Yammacin Nijeriya ne za su fito da shugaban kasa a zaben shekara ta 2023.
Cif Jide Awe, ya bayyana haka ne, yayin da aka gayyace shi zuwa wani gidan rediyo na Voice FM a Ekiti, inda ya yi tsokaci
game da zaben shekara ta 2023, da dakarun Amotekun, tare da sukar kalaman kungiyar Miyettti-Allah.
Ya ce shugaban kasar da za a yi a shekara ta 2023, zai fito ne daga Kudu maso Yamma, saboda tsarin karba-karba da aka saba aiki da shi a Nijeriya.
Awe ya kara da cewa, ba siyasa ta sa aka kafa jami’an tsaro na Amotekun ba, ya na mai kalubalantar kugiyar Miyettti-Allah da cewa ba su ke bada mulki ba.
Cif Awe ya kuma jinjinawa gwamnonin jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya da su ka kafa jami’an tsaron su, domin tsare rayuka da dukiyoyin wadanda ke yankin.