A wani mataki na ci gaba da neman goyon bayan al’umma kungiyar G20 Dan Galadiman Duguri ta kai wa jigo a jam’iyyar PDP Alhaji Abubakar Mai Doki ziyarar girmamawa.
Shugaban kungiyar Komared Ishaq Maijinka, ya ce wannan ziyara ya zama wajibi ta la’akari da mihammancin samun goyon bayan irin su Abubakar Mai Doki a tafiyar ta G20 Dan Galadiman Duguri.
Konared Ishaq Maijinka ya ce bisa cancantar Abubakar Mai Doki kungiyar ta G20 Dan Galadiman Duguri ta bashi mukamin babban jami’i mai sanya ido kan aikin kungiyar a kananan hukumomi 7 na shiyyar Bauchi ta kudu a jihar Bauchi.
A jawabin san a godiya Alhaji Abubakae Mai Doki ya nuna farin ciki da wannan mukami da aka bashi sai ya sha alwashin yin aiki tukuru domin ganin kungiyar ta G20 Dan Galadiman Duguri ta cimma nasara a wannan kyakykyawar manufa ta ta.
Suma wasu daga cikin shugabannin kungiyar da suke cikin tawagar da ta kai ziyarar, da suka kunshi mai magana da yawun kungiyar Hassan Usman Ajiyan Sarkin Bindigar Bauchi, da shugabar mata ta kungiyar, da jami’ar kula da harkokin mata ta kungiyar da kuma jami’ar kula da ayyukan na musamman ta kungiyar duk sun nuna godiya ne da yadda ake tarbi tawagar ta su da hannu bibbiyu sai suka yi fatar tafiyar za ta cimma nasara.