Cibiyar tabbatar da shari’ar Musulunci ta jihar Kano Hisbah, ta gayyaci dattijuwar Ba’Amurkiyar da ta je Kano a kan auren masoyin ta Sulaiman Isa zuwa ofishin su domin amsa tambayoyi.
Dattijuwar mai shekaru 45 kuma mahaifiyar ‘ya’ya biyu mai suna Jeanine Delsky, ta isa Panshekara ne domin haduwa da saurayin ta Sulaiman, wanda su ka hadu a kafar sada zumunta ta Instagram.
Yayin tabbatar da gayyatar, Sulaiman Isa ya ce sun fara zuwa ofishin Hisbah na Panshekara ne kafin su gangara zuwa helkwatar cibiyar.
Ya ce babu wani abu a kan gayyatar, kawai an ba su shawarwari ne kuma sun ji daga mahaifin sa, sun kuma tabbatar ta na da niyya mai kyau a kan sa, don haka an shawarce shi ya rike addinin shi bayan sun koma Amurka.
Masoya biyun dai sun hadu ne a dandalin Instagram, inda su ka fara musayar hotuna tare da soyayyar yanar gizo, yayin da Deslky ta ce ta yi soyayya da mutane masu tarin yawa a yanar gizo amma ba ta samu tamkar Isa ba.