Home Labarai Hadi Sirika: EFCC Ta Tsare Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya

Hadi Sirika: EFCC Ta Tsare Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya

26
0
Hadi Sirika
Hadi Sirika

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa
zagon-ƙasa EFCC ta ce ta kama tsohon Ministan Ma’aikatar
Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almundahana.


Shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ne ya tabbatar da hakan a ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja. Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za su gurfanar da Sirika tare da ɗan’uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahanar N8.06 bn.

Rahotanni sun ce zargin da ake yi wa tsohon ministan yana da alaƙa da yadda ya bayar da kwangiloli ga ɗan’uwansa Abubakar Siriki kan aiwatar da wasu ayyuka na Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama.

Ɗaya daga cikin kwangilolin ita ce wacce ya bai wa kamfanin Engirios Nigeria Limited na ɗan’uwan nasa a watan Agustan 2022 domin gina tashar jirgin sama a filin jirgin saman Katsina a kan kimanin N1.3bn Hadi Sirika, wanda ya shafe kusan shekaru takwas yana riƙe da muƙamin minista a zamanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ya jawo ce-ce-ku-ce lokacin da ya ƙaddamar da jirgin saman Nijeriya, wato Nigeria Air suna dab da sauka daga mulki.

Ana zargi an yi rufa-rufa wurin ƙaddamar da Nigeria Air, ko da yake ya sha musanta hakan.

Leave a Reply