Home Labarai Unai Emery Ya Sabunta Kwantaraginsa A Aston Villa

Unai Emery Ya Sabunta Kwantaraginsa A Aston Villa

112
0
5334961
5334961

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa da ke Ingila, Unai
Emery ya sabunta yarjejeniyar zamansa a kungiyar har zuwa
shekarar 2027.


Emery, ya karbi ragamar jagorancin kungiyar a watan Nuwamban 2022 lokacin da kungiyar ke matsayin na 17 a teburin Firimiyar Ingila. Aston Villa ta yaba da yadda kocin mai shekaru 52 ya sauya kungiyar cikin kankanin lokacin, inda yanzu ta ke a matsayi na hudu a gasar.

Idan kungiyar ta karkare a matsayin da ta ke, hakan zai ba ta damar buga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa. Unai Emery, ya horas da kungiyoyi irin su Sevilla, Villarreal, Arsenal, PSG da sauransu kafin zama kocin Aston Villa.

Leave a Reply