Home Labaru Ra’ayi: Zanga-Zangar Da PDP Za Ta Shirya Ba Za Ta Yi Armashi...

Ra’ayi: Zanga-Zangar Da PDP Za Ta Shirya Ba Za Ta Yi Armashi Ba – Timi Frank

329
0
Ra’ayi: Zanga-Zangar Da PDP Za Ta Shirya Ba Za Ta Yi Armashi Ba - Timi Frank
Ra’ayi: Zanga-Zangar Da PDP Za Ta Shirya Ba Za Ta Yi Armashi Ba - Timi Frank

Tsohon jigo a jam’iyyar APC Kwamred Timi Frank, ya ce shirin da ‘yan jam’iyyar PDP ke yi na gudanar da zanga-zanga game da hukuncin da kotun koli ta yi a kan zaben gwamnan jihar Imo ba zai yi tasiri ba.

 Kwamred Timi Frank, ya ce ya na ganin zanga-zangar da PDP za ta shirya ba za ta tasiri ba domin an makara.

 A cewar sa, PDP ta makara wajen shirya zanga-zangar, domin ba ta yi zanga-zanga a lokacin da aka tsige Walter Onnoghen daga kan kujerar shugaban Alkalan Nijeriya ba.

Ya ce jam’iyyar PDP ta yi sake a lokacin da kotun koli ta yi watsi da karar Atiku Abubakar a kan zaben shekara ta 2019, amma su ka yi shiru.