Home Labarai ‘Yan Majalisar Dokokin Cross River Sun Tsige Shugaban Majalisar

‘Yan Majalisar Dokokin Cross River Sun Tsige Shugaban Majalisar

70
0
Elvert Ekom Ayambem
Elvert Ekom Ayambem

‘Yan majalisar dokokin jihar Cross River sun tsige shugaban majalisar Rt. Hon. Elvert Ekom Ayambem.

A yau Laraba ne ‘yan majalisar 17 daga cikin 25, suka amince da tsige shugaban na su sakamakon zargin sa da ɓarnatar da kuɗi.

Tun a ranar Talata ne ‘yan majalaisar suka fara yaunƙurin tsige Rt. Hon. Elvert Ekom Ayambem,

inda kusan ‘yan majalisar 20 suka goyi bayan ƙudirin tsige ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Ikom 2.

A watan Yunin 2023 ne aka zaɓi Rt Hon Elvert Ayambem, a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar ta 10.

Leave a Reply