Home Home Tinubu Zai Fuskanci Bore Kan Tsayar Da Akpabio A Matsayin Shugaban Majalisa

Tinubu Zai Fuskanci Bore Kan Tsayar Da Akpabio A Matsayin Shugaban Majalisa

76
0

Zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jam’iyyar APC, sun kawo karshen dambarwar neman shugabancin majalisar tarayya ta 10 da za a kaddamar nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Rahotanni sun ce, Tinubu da gwamnonin a karshe sun tsaida tsohon ministan kula da harkokin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa, sannan sun zabi Sanata Barau Jubrin daga jihar Kano a matsayin mataimaki.

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa, Tinubu ya kuma tsaida Tajudden Abbass daga jihar Kaduna a matsayin sabon Kakakin majalisar wakilai.

Mukamin mataimakin shugaban majalisar wakilai kuma an ba dan majalisa Benjamin Kalu daga jihar Abia.

Leave a Reply