Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce tsarin biyan kudin makaranta ga daliban sakandiri da ma’aikatar ilimin jihar ta bullo da shi ya ci karo da tsare-tsaren gwamnatin jihar.
A wata sanarwa da mataimakin gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye, ya sanya wa hannu gwamnan Nasir El-Rufa’I, ya bayyana tsarin ilimi kyauta a matsayin babban burin da gwamnatin sa ta sanya a gaba.
Sanarwar ta ce gwamatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga daliban sakandire a fadin jihar Kaduna.
A baya dai ma’aikatar ilimin jihar Kaduna ta fitar da sanarwar da ke cewa daliban sakandire a jihar za su fara biyan kudin makaranta, sai dai a yanzu gwamna El-rufa’i, ya ce daliban furamare da sakandiri a jihar za su yi karatu ne kyauta.