Home Home Rayuwa Za Ta Tsaya Cak Matukar Gwamnati Ba Ta Samar Da Hanyoyin...

Rayuwa Za Ta Tsaya Cak Matukar Gwamnati Ba Ta Samar Da Hanyoyin Samun Sauki Ba – Amnesty

78
0

Kungiyar kare hakkin bil’adama Amnesty International, ta ce cire tallafin man fetur ba tare da matakan rage radadi ga talakawa ba zai jefa akasarin jama’a cikin karin kuncin talauci.

Ta ce rayuwar talakawa za ta iya tsayawa cak matukar gwamnati ba ta cika alkawarin samar da hanyoyin saukaka wa ‘yan kasa ba, domin tuni farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabo, musamman a yadda sufuri ke shafar rayuwar tattalin arzkin kasa.

Daraktan kungiyar a Nijeriya Isa Sunusi, ya ce sun lura duk muhimman sassan rayuwar ‘yan Nijeriya ta na da alaka da man fetur.

Talakawa dai sun so fakewa da kungiyar kwadago domin mara baya ga yajin aiki ko matsawa gwamnati lamba ta sake matsaya, amma zuwan ‘yan kwadagon fadar fadar shugaban kasa ya sa su ka jingine matakai masu tsauri zuwa doguwar tattaunawa.

Leave a Reply