Home Labaru Majalisar Wakilai Ta Nemi A Kammala Aikin Madatsar Ruwa Ta Faki A...

Majalisar Wakilai Ta Nemi A Kammala Aikin Madatsar Ruwa Ta Faki A Jihar Kaduna

139
0

Majalisar Wakilai ta bukaci Ma’aikatar albarkatun ruwa da ta dauki dukkan matakan da suka wajaba domin kammala aiki gyaran madatsar ruwa da ke garin Faki a karamar Hukumar Ikara ta jihar Kaduna.

Bukatar hakan na kunshe a cikin wani kudiri da dan Majalisar dake wakiltar mazabar Ikara da Kubau, Dr. Hamisu Ibrahim Kubau, ya gabatar a zaman majalisar na ranar al’hamis.

Da yake gabatar da Kudirin Dr. Hamisu Ibrahim Kubau, ya ce tun a shekara ta 2003 ne aka bada kwangilar gyaran madatsar ruwa ta Paki, sannan dan kwangilar ya yi watsi da aikin ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Dan majalisar ya ce rashin kammala aikin yana mutukar shafar kokarin gwamnatin tarayya na aiwatar da tsarin ta na fadada tattalin arziki ta bangaren ayyukan gona domin bunkasa samar da abinci tare da wadata kasa da abincin.

Ya ce idan aka kammala aikin gyaran dam din na Paki zai taimaka wa alumomin yankin su cimma bukatun su ta fannin samar da amfanin gona Mai inganci kamar su shinkafa, da alkama, da kayan Lambu da Kuma kiwon kifi.

Har ila yau Dr. Hamisu Ibrahim ya bukaci majalisar ta dauki mataki ta hanyar tabbatar da ganin an kammala aikin, idan Kuma Kanfanin ba za iya ba a kwace a baiwa Wanda zai iya yadda al’ummar yankin za su amfana.

Leave a Reply