Home Labaru Kiwon Lafiya Kula Da Lafiya:  Yara Miliyan Ɗaya Na Mutuwa Duk Shekara A Najeriya...

Kula Da Lafiya:  Yara Miliyan Ɗaya Na Mutuwa Duk Shekara A Najeriya -Ministan Lafiya

113
0

Ministan Lafiya a Najeriya, Farfesa Ali Muhammad Pate ya ce kimanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar na mutuwa duk shekara sakamakon cututtuka ciki har da waɗanda rigakafi ke samar da kariya daga kamuwa da su.

Ministan ne ya bayyana haka, inda ya ce kashi 70 cikin 100 na mace-macen ana iya kare su, ya ce akwai kimanin mace-macen yara miliyan ƴan ƙasa da shekara biyar duk shekara a ƙasar nan, kashi 70 na mace-macen sakamakon cututtuka kamar mashaƙo da ƙyanda da nimoniya da ake iya kandagarkinsu ta hanyar yin rigakafi.

Farfesa Pate ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ya bijiro da tsare-tsare da za su shafi rayuwar talaka inda ya ce zuba hannun jari a ɓangaren lafiya na daga cikinsu.

Ya ce ana samar da matakai da dama na magance zazzabin cizon sauro a Najeriya ciki har da amfani da gidan sauro da rigakafi.

A cewarsa, Najeriya a shirye take ta samar da alluran rigakafin zazzabin cizon sauro a ƙasar ba da daɗewa ba.

Leave a Reply