Home Labaru Kotu Ta Maida Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Kan Mukamin Sa

Kotu Ta Maida Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Kan Mukamin Sa

99
0

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta maida
Mahadi Aliyu Gusau a kan matsayin sa na mataimakin
gwamnan jihar Zamfara.

Mahdi Aliyu Gusau da jam’iyyar PDP, sun shigar da ƙara ne a kan hanyar da majalisar dokoki ta jihar ta bi wajen tsige shi daga muƙamin sa a watan Fabrairu na shekara ta 2022.

Da yake zartar da hukuncin, mai shari’a Inyang Ekwo ya ce kwamitin bincike da tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ya kafa ya saɓa doka.

Alƙalin dai ya bada umarnin maida Mahadi Aliyu Gusau a kan muƙamin mataimakin gwamna tun daga ranar da ya shigar da ƙara a watan Yuli na shekara ta 2021.

Mai shari’a Inyang Ekwo, ya kuma kawar da dukkan matakai da hanyoyin da aka bi wajen tsige mataimakin gwamnan lokacin da ƙarar ta ke a gaban kotun.

Leave a Reply