Kotun sauraren korafe-korafen zabe da ke a Kaduna, ta dage zaman ta zuwa ranar 25 ga watan Yuli na shekara ta 2019, domin sauraren jawabin karshe daga bakin lauyoyi a shari’ar Sanata Shehu Sani da Sanata Uba Sani.
Sanata Shehu Sani dai ya na kalubalantar nasarar da Uba Sani ya samu a zaben da ya gabata, inda ya bukaci kotu ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, lauyan sanata Shehu Sani Morris A. Odeh, ya ce an gama sauraren shaidu saboda sanata Uba Sani ya kasa gabatar da shaida ko guda.
Odeh ya kara da cewa, sanata Shehu Sani ya gabatar da shaidu biyu a lokacin da ake sauraren shari’ar, amma sanata Uba sani ya gaza gabatar da shaida ko guda.
Ya ce abin da ake ciki yanzu shi ne, za su koma ranar 25 ga watan Yuli don su gabatar da jawabin karshe, daga nan su saurari hukuncin kotu.
You must log in to post a comment.