Home Labarai Jirgin Yaƙin Soji Ya Yi Luguden Wuta Kan Mutane Bisa Kuskure A Neja

Jirgin Yaƙin Soji Ya Yi Luguden Wuta Kan Mutane Bisa Kuskure A Neja

348
0

Wani jirgin yaƙi na rundunar sojin saman Nijeriya, ya yi kuskuren kashe kananan yara shida a jihar Neja.

Lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Kurebe da ke ƙaramar hukumar
Shiroro, yankin da ya dade cikin rashin tabbas, saboda yawan
hare-haren ‘yan ta’adda.

Kakakin gamayyar ƙungiyoyin yankin Salis Sabo ya bayyana
haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jirgin ya yi
kuskuren taɓa kananan yaran ne a lokacin da su ke kan hanyar
komawa gida daga wurin da su ke zuwa ɗebo ruwa.

Ya ce biyu daga cikin yaran da lamarin ya shafa marayu ne,
waɗanda iyayen su su ka mutu a wani harin da ‘yan bindiga su
ka kai wa ƙauyen.

Leave a Reply