Home Labarai Jihohin Najeriya 10 Kacal Sun Fi Kasashen Afirka Girma, Inji Osinbajo

Jihohin Najeriya 10 Kacal Sun Fi Kasashen Afirka Girma, Inji Osinbajo

152
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce ba daidai ba ne a rika kwatanta yanayin tattalin arzikin Nijeriya da na sauran kananan kasashen Afirka.

Yemi Osinbajo, ya ce akalla jihohi 10 na Nijeriya kacal su na da karfin tattalin atrzikin da ya kere na wadancan kasashe.

Ya ce rahotanni marasa dadi da ke fitowa daga Nijeriya ba su ke nuna gaskiyar yadda kasar nan baki daya ta ke ba, domin kasa ce mai girman kasa, don haka ba ilahirin Nijeriya ke fama da munanan abubuwan da ake gani a gidajen talabijin da gidajen jaridu ba.

Osinbajo ya cigaba da cewa, ya na da kyau kasashen duniya su fahimci irin yawan ‘yan Nijeriya da kuma girman fadin kasar ta, domin su fahimci girman kalubalen da ta ke fuskanta.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyyana haka ne, lokacin da ya ke amsa tambayoyin daliban makarantar kasuwanci ta Harvard da su ka ziyarce shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Leave a Reply