Home Home Haramar 2023: Hukumar Zabe Ta Ce Babu Wanda Zai Kada Kuri’a Sai...

Haramar 2023: Hukumar Zabe Ta Ce Babu Wanda Zai Kada Kuri’a Sai Ya Na Da PVC 

30
0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC Ta Jaddada Cewa Babu Wanda Za a Bari Ya Jefa Kuri’a a Babban Zaben Kasa Dake Tafe Sai Ya Nuna Katin Zabe Na Dindindin.

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmud Yakubu Ne Ya Bayyana Haka a Lokacin Kaddamar Da Taron Sabbin Kwamishinonin Zabe Na Hukumar, Wanda Aka Gudanar a Legas.


Farfesa Mahmud Yakubu Ya Bukaci Al’Ummar Kasar Da Su Yi Watsi Da Jita-Jitar Da Ke Cewa Mutum Na Iya Kada Kuri’a a Ranar Zabe Ba Tare Da Katin Na Pvc Ba.
Ya Ce Sashe Na 47 Sakin Layi Na (1) Na Dokar Zabe Ta 2022 Ta Ce Duk Wanda Zai Kada Kuri’a Zai Gabatar Da Katin Zabensa Ga Jami’In Zabe Domin Tantancewa a Rumfar Zaben Da Ya Yi Rajista.


Saboda Haka Ya Ce Dokar Ba Ta Sauya Ba, Wajibi Ne Ga Duk Wanda Zai Kada Kuri’a Ya Gabatar Da Katin Zaben Sa Ga Jami’An Zabe.