Home Labaru Gwamnonin Arewa Sun Garzaya Ibadan Domin Ganin Halin Da ‘Yan Arewa Ke...

Gwamnonin Arewa Sun Garzaya Ibadan Domin Ganin Halin Da ‘Yan Arewa Ke Ciki

458
0

Biyo bayan kammala taron Tsaro a Jihar Kaduna tsakanin Gwamnonin Arewa da Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro da ma manyan Hafsoshin Jami’an tsaro.

Gwamnonin sunyi tsinke zuwa Ibadan Inda wani rikicin ƙabilanci ya barƙe tsakanin Yarbawa da Hausawa a Juma’ar da ta gabata.

Cikin Gwamnonin da suka tafi Ibadan akwai Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, Gwamnan Jihar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan Jihar Kebbi Senator Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje sai kuma Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Lolo inda suka nufi Garin Ibadan Jihar Oyo domin duba halin da ‘Yan Arewa Hausawa suke ciki a Jihar ta Oyo.

Zamu Kawo Maku Cikakken Bayani Insha Allah yadda tafiyar ta kaya.