Home Labaru Gwamnati Ta Amince Da Sabbin Manufofin Bunkasa Samar Da Motoci A Nijeriya

Gwamnati Ta Amince Da Sabbin Manufofin Bunkasa Samar Da Motoci A Nijeriya

98
0

Gwamnatin Tarayya ta amince da sabbin manufofin amfani da
mota, wadanda ke kunshe a sabon Tsarin Bunkasa
Masana’antar Kera Motoci ta Kasa ta shekara ta 2023.

Ministan Masana’antu da Ciniki da Zuba Jari Otunba Niyi Adebayo ya gabatar da takardar ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Hukumar NADDC dai ta bullo da sabon shirin da za a yi amfani da karfin tuwo wajen tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu kawo yanzu a masana’antar kera motoci ta Nijeriya.

Sabbin manufofin da aka amince da su dai, za su bada damar haɓaka adadin motocin da ke kerawa a cikin gida, wanda ya kai kashi 40 cikin 100, da samun kashi 30 cikin 100 na motocin lantarki da ake samarwa a cikin gida, da kuma samar da guraben ayyukan yi miliyan daya.

Leave a Reply