Home Labaru Fiye Da Mutane 100 Sun Mutu Cikin Sa’o’i 48 A Hare-Haren Jihar...

Fiye Da Mutane 100 Sun Mutu Cikin Sa’o’i 48 A Hare-Haren Jihar Fulato- Maren

59
0

Wasu bayanai sun nuna cewa, a cikin sa’o’i 48 hare-haren
‘yan ta’adda sun hallaka mutanen da yawan su ya haura 100 a
wasu sassan jihar Filato, a daidai lokacin da gwamnatin jihar
ta sanya dokar takaita walwalar jama’a a yankunan da hare-
haren ke faruwa.

Dan Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Mangu da Bokkos Solomon Maren, ya ce mahara na ci-gaba da kai hare- hare a kan kauyuka tare da kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce hare-haren sun fi tsananta a yankin da ya ke wakilta, wanda ke nuna bukatar daukar mataki duba da yadda mutanen kauyukan da ake kai hare-haren ke rayuwa cikin fargaba.

Dan Majalisar ya ce a cikin sa’o’i 48, sai da hare-haren su ka salwantar da rayukan mutane fiye da 100, wanda ke nuna mutuwar mutanen da yawan su ya haura 200 a makamantan hare-haren cikin watanni 2 da su ka gabata.

Ya ce maharan su na kone gidaje da gonaki da shagunan da ake adana amfanin gona, ya na mai kakkausar suka ga matakan da gwamnati ke dauka a kokarin yaki da matsalar tsaron da yankuna da dama ke fama da ita a Nijeriya.

Leave a Reply