Home Home Cire Tallafin Man Fetur Ba Nan Take Zai Fara Aiki Ba, Sai...

Cire Tallafin Man Fetur Ba Nan Take Zai Fara Aiki Ba, Sai Karshen Watan Yuni – Tinubu

96
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi karin haske game da kalaman sa na cire tallafin man fetur a fadin Nijeriya.

Wata sanarwa da masu taimaka masa ta fuskar yada labarai su ka fitar, ta ce furucin da Shugaba Bola Tinubu ya yi cewa tallafin man fetur ya kare ba wani abu ne sabo da gwamnatin shi ta kirkira ba.

Sanarwar ta ce Tinubu ya sake nanata halin da ake ciki ne, duba  da cewa kasafin kudin tallafin man fetur da gwamnatin Buhari ta tsara ta amince da tallafin ne kawai a rabin farkon shekara.

Wannan dai ya na nufin cewa, a karshen watan Yuni na shekara ta 2023, Gwamnatin Tarayya za ta kasance ba ta da wani tanadin kudade domin ci-gaba da biyan tallafin man fetur.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya cewa, kada su shiga wani firgici ko damuwa, domin cire tallafin ba zai fara aiki nan take ba.

Leave a Reply