Home Labarai Birtaniya Ta Dakatar Da Daukar Ma’Aikatan Lafiya Daga Najeriya

Birtaniya Ta Dakatar Da Daukar Ma’Aikatan Lafiya Daga Najeriya

107
0

Gwamnatin Birtaniya ta dakatar da hukumomin kasar daga
daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga Nijeriya.

Yanzu haka dai, Nijeriya ta shiga sahun kasashen duniya da ke fama da gagarumar matsalar karancin ma’aikan lafiya, kamar yadda kudnin Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna.

A cikin watan Maris da ya gabata, hukumar lafiya ta duniya, ta wallafa wani kundi mai kunshe da sunayen kasashen duniya 55 ciki har da Nijeriya, wadanda ke ci-gaba da fama da karancin ma’aikatan kiwon lafiya.

Gwamnatin Birtaniya, ta ce ya kamata a ba Nijeriya da wasu kasashen da ke cikin bakin kundin fifiko wajen bunkasa bangaren kiwon lafiyar su, tare da shata layin da zai hana daukar ma’aikatan su na kiwon lafiya a matakin kasa da kasa.

Da dama daga cikin likitoci da sauran ma’aikatan jinya dai sun fice daga Nijeriya bayan sun samu aiki a kasasahen ketare, inda su ke ganin sun fi samun kulawa fiye da kasar su ta asali.

Leave a Reply