Home Home Bidiyon Dala Muhuyi Zai Binciki Ganduje

Bidiyon Dala Muhuyi Zai Binciki Ganduje

77
0

Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya sha alwashin bincikar tsohon Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje game da bidiyon da aka gan shi ya na cusa kuɗi a aljihun sa.

Muhuyi Rimin Gado wanda Ganduje ya cire bayan sun samu saɓani, ya ce binciken ya zama wajibi.

Ya ce lokacin da ya na ofis sun fara bincike, amma akwai tarnaƙi kasancewar gwamna mai ci ya na da kariyar shari’a.

Rimin Gado ya cigaba da cewa, amma yanzu tunda Ganduje ya sauka kariya ta sauka, don haka hukuma za ta yi abin da ya dace.

Leave a Reply