Home Home Ba Zan Daina Rusau Da Korar Ma’aikata Ba, Har Sai Na Bar...

Ba Zan Daina Rusau Da Korar Ma’aikata Ba, Har Sai Na Bar Mulki – El-Rufa’i

81
0

Gwamnan jihar Kaduna mai barin gado Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai daina korar bara-gurbin ma’aikata da kuma rusa haramtattun gine-gine ba har sai ya bar mulkin jihar.

El-Rufai ya bayyana haka ne, washegarin da ya kwace izinin mallaka tare da sanya alamar rusa wasu kadarori 9 mallakin tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.

Da ya ke bayani a wajen taron kaddamar da littafin da wani dan jarida Emmanuel Ado ya rubuta a kan ayyukan sa, mai suna El-Rufa’i ya ce har zuwa ranar karshen mulkin shi ba zai daina kawar da bara-gurbin mutane da sauran miyagun abubuwa ba.

Ya ce duk abin da ya ga bai dace ba zai kawar da shi, don kada su zama matsala ga sabon gwamnan da zai karbi mulki bayan ya kammala na shi.

Leave a Reply