Home Labaru An Kashe Mutane Biyar Da Ƙona Gidaje Yayin Rikicin Manoma Da Makiyaya...

An Kashe Mutane Biyar Da Ƙona Gidaje Yayin Rikicin Manoma Da Makiyaya A Ogun

122
0

An kashe aƙalla mutane biyar, tare da kone gidaje da gonaki da dama yayin wani rikicin makiyaya da manoma a Imeko-Afon da ke jihar Ogun.

Wata majiya ta ce, rikicin ya faru ne bayan wasu ‘yan watanni da faruwar makamcin sa a kauyen Yewa da ke jihar.

Bayanai sun ce rikicin ya faro ne tun daga ranar Larabar da ta gabata, lokacin da mutanen wani gari da ake kira Aworo a ƙaramar hukumar Yewa su ka fatattaki makiyaya zuwa wani ƙauye da ake kira Idif, tare da kashe uku daga cikin su.

Al’ummomin yankin, sun zargi makiyayan ne da lalata gonakin su da wuraren shan ruwa sakamakon ƙyale shanun su su na kiwo a fili.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce babu wanda aka kama ya zuwa yanzu.