Home Labaru An Ci Tarar Chelsea Fam 25,000, Bayan ‘Yan Wasa Sun Kalubalanci Jan...

An Ci Tarar Chelsea Fam 25,000, Bayan ‘Yan Wasa Sun Kalubalanci Jan Katin Reece

102
0

Chelsea za ta biya tarar fam dubu 25, bayan ta kasa tsawatarwa ‘yan wasanta, a lokacin da aka ba Reece James jan kati a karawa da Liverpool cikin watan Agusta da ya gabata.

Alkalin wasan Anthony Taylor, ya kori James daga karawar, wanda ya sawa kwallo hannu a kan layin raga, inda daga bisani kuma aka bada fenaritin da Mohammed Salah ya buga ya farke kwallon da Chelsea ta zura a gasar Premier League.

‘Yan wasan Chelsea sun harzuka da hukuncin Taylor, inda suka ce kwallon ya fara bugar cinyar dan wasan tawagar Ingila kafin ya taba hannun sa.

Hukuncin da aka yanke shine, James ba zai buga wa Chelsea gasar Premier League da za ta fafata da Aston Villa ranar Asabar a Stamford Bridge ba.