Home Labaru Kasuwanci Abin Murna: Bankin CBN Ya Kafa Kwamitin Farfado Da Masaku 50 A...

Abin Murna: Bankin CBN Ya Kafa Kwamitin Farfado Da Masaku 50 A Cikin Shekaru 4

513
0

Babban bankin Nijeriya CBN, ya kafa kwamitin farfado da masakun Nijeriya.

Yayin da ya ke kaddamar da kwamitin a Abuja, gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, ya ce manufar kwamitin ita ce farfado da masaku 50 a cikin shekaru 4 masu zuwa.

Ya ce kwamitin zai kasance ya maida hankali wajen sake farfado da masakun da aka mance da su a Nijeriya.

Haka kuma, bunkasa noman auduga ya na daga cikin ayyukan kwamitin, ta yadda audugar za ta wadaci ko ina a fadin Nijeriya.

Godwin Emefiele, ya ce bankin CBN zai hada hannu da hukumar kwastam domin dakile fasa-kwauri, tare da samar da kyakkyawan yanayin gudanar da sana’ar ba tare da an tsawwala haraji ba. Wasu daga cikin gwamnonin da su ka halarci taron kaddamar da kwamitin kuwa sun hada da Abdullahi Ganduje na jihar Kano, da Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe da kuma mataimakin gwamnan jihar Kaduna Barnabas Bala Bantex.

Leave a Reply