Tsohon shugaban hukumar (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa ‘yan majalisan Nijereiya na matsinlamba ga jami’an gwamnati wajen yin cushe a kasafin kudi.
Farfesa Jega ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a taron ‘Horar da canjin dabi’un cin hanci wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka (ICPC) ta shirya a Abuja.
Ya bayyana cin hanci a ma’aikatun gwamnati a matsayin babban cikas ga ci gaban Nijeriya tare da sukar matsalolin da manyan jami’ai ke fuskanta musamman daga bangaren majalisa.
Ya tunatar da yadda wasu ‘yan majalisar suka yi yunkurin yin tasiri a kan kasafin kudi da kuma tabbatar da kwangiloli,
wanda hakan ya kawo cikas ga kokarin jami’an gwamnati na tabbatar da gaskiya.