Jami’ai a Lebanon sun ce aƙalla ma’aikatan agaji 15 aka kashe a wani hari da Isra’ila ta kai a arewa maso gabashin ƙasar.
Harin da aka kai birnin Baalbek ya sauka a wata cibiyar tsaron gwamnati wadda ba ta da alaƙa da Hezbollah.
Gwamnan lardin, Bachir Khodr, ya ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da shugaban jami’an tsaro na civil defence a yankin, Bilal Raad.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta yi Alla-wadai da mummunan harin.
Sojojin Isra’ila ba su ce uffan ba kan harin, waɗanda ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta kwatanta da mai muni.
Rahotanni sun bayyana cewa sabon harin Isra’ila a ƙauyukan da ke kudancin Beiruta ya lalata gine-gine.