Home Labarai Kyautar Globe Soccer: Messi, Ronaldo, Lookman Na Cikin ‘Yan Takarar A Bana

Kyautar Globe Soccer: Messi, Ronaldo, Lookman Na Cikin ‘Yan Takarar A Bana

199
0
91df076179bc0ebb
91df076179bc0ebb

An saka sunan dan wasan Najeriya, Ademola Lookman a cikin wadanda aka zaba don samun kyautar gwarzon dan wasan maza na shekarar 2024, wanda kungiyar Globe Soccer take bayarwa kuma hukumar wasanni ta Dubai ke karbar bakunci.

Globe Soccer Awards ta sanar da hakan a ranar Alhamis a wata sanarwa da ta saka a shafinta na X.

Tsohon dan wasan Leicester wanda yanzu haka tauraruwar sa ke haskawa a Atalanta ta kasar Italiya, ya yi fice a ‘yan shekarun nan tare da Atalanta a Seria A.

Lookman ya shiga cikin manyan taurarin kwallon kafa, Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, Kylian Mbappé, da Erling Haaland na daga cikin jerin ‘yan wasan da ka iya lashe kyautar.

Dan wasan Manchester City, Phil Foden, Jude Bellingham na Real Madrid, da Cole Palmer na Chelsea suna wakiltar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Ingila.

Messi da Ronaldo sun sake fitowa a cikin jerin sunayen duk da cewar su na tunkarar shekarun su na karshe na taka leda.

Robert Lewandowski na Barcelona da Leroy Sané na Bayern Munich, tare da Bukayo Saka, suna cikin jerin sunayen.

Globe Soccer Awards ta ce duk dan wasan da ya fi samun yawan kuri’u zai kasance a cikin jerin ‘yan wasa uku da za su shiga mataki na gaba wajen neman lashe kyautar.

Leave a Reply