Home Labarai Sammacin Kama Netanyahu: Biden Ya Soki Matakin   Kotun ICC

Sammacin Kama Netanyahu: Biden Ya Soki Matakin   Kotun ICC

23
0
U.S. President Joe Biden's campaign event in Atlanta
U.S. President Joe Biden's campaign event in Atlanta

Shugaba Joe Biden na Amurka ya kira sammacin kama firaministan Isra’ila da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ba da da abin takaici.

ICC ta ce ta bayar da sammacin Benyamin Netanyahu kan zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza.

Tuni ‘yan siyasa a Isra’ila suka fara martani kan hukuncin, ciki har da tsohon firaministan ƙasar, Naftali Benneth, wanda ya ce an gina ilahirin sammacin a kan ƙarya.

Mista Benneth ya ce Wannan abin dariya ne ma, za mu maida martani, ba za mu zuba ido haka nan a cuce mu ba..

Da wannan sammacin na kotun ICC ƙasashe mambobin kotun na da damar kamawa tare da tsare Mista Netanyahu idan ya shiga ƙasashen su.

Leave a Reply