Roger Federer ya yi jinjina ta musamman ga Rafael Nadal wanda ke sanar da ritayarsa daga fagen Tennis inda ya bayyana takwaran nasa na Spain a matsayin wanda ya haska ƙwallon Tennis tare da kai gasar wani mataki a duniya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Federer mai shekaru 43 ya yi fatan alkhairi ga Nadal tare da jinjina kan tarihin da ya kafa tsawon shekaru.
Roger Federer da Rafael Nadal sun shafe shekara 15 suna dabi a tsakanin su wanda ya zama mafi kayatarwa a duniyar Tennis.
Nadal mai shekara 38 wanda ya lashe kyautar Grand Slam 22 a tsawon lokacin da ya ɗauka ya na haskawa a fagen Tennis,.
ya kawo ƙarshen haskawar sa a fagen na Tennis ne bayan wakiltar Spain a gasar Davis Cup da ke gudana a Malaga.
Ritayar Nadal na zuwa ne shekara biyu bayan Federer ya yi tasa ritayar a shekarar 2022, wanda shi ma ya lashe kyautar Grand Slam 20 a tsawon lokacin da ya shafe ya na haskawa a fagen na Tennis.