Home Labarai Yakar Lakurawa: Ministan Tsaro Ya Ce Sojoji Sun Shirya

Yakar Lakurawa: Ministan Tsaro Ya Ce Sojoji Sun Shirya

29
0
download (38)
download (38)

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun kammala shirye-shiryen murƙushe ‘yan ƙungiyar Lakurawa, da ke addabar jama’a a waɗansu jihohin arewa maso yamma.

Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan ƙungiyar suka kai hari a makon daya wuce a jihar Kebbi inda suka hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.

Ministan tsaro na Najeriya, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana ƙudurin rundunonin sojin ƙasa na tunkarar matsalar tsaron ta Lakurawa da ta kunno kai kwanannan, a hirar sa da manema labarai.

Ministan ya ce manyan hafososhin tsaron Najeriya sun riga sun fitar da wani tsari na musamman da zai hana ‘yan Lakurawan yin tasiri a arewacin Najeriya.

Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasa da na ruwa da na sama sun gana da babban hafsan tsaro Janar Christopher Musa, inda suka yi masa bayani kan matakan da suka shirya ɗauka kan wannan ƙungiya.

Leave a Reply