Home Labaru Yadda Boko Haram Ta Yi Wa Sojojin Nijeriya Kwanton – Bauna

Yadda Boko Haram Ta Yi Wa Sojojin Nijeriya Kwanton – Bauna

1013
0

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojin ta biyar kusa da garin Jakana mai nisan kilomita 30 daga birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Larabar da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafukan ta na sada zumunta, ta ce sojojin da su ka mutu sun hada da Kanar da Kyaftin da wasu sojoji uku a wani kwanton-bauna da mayakan su ka yi musu yayin da su ke tafiya zuwa Damaturu daga Maiduguri.

Rundunar sojin, ta ce tun farko mayakan Boko Haram ne su ka yi kokarin kai hari sansanin sojoji na Bataliya ta 212 da ke Jakana domin satar kayan yaki da su ke tsananin bukata.

Mayakan dai sun je ne da misalin karfe 7 saura kwata na yamma, a cikin motocin igwa guda bakwai, kuma an fafata da su sosai yayin da su ke son kutsawa sansanin da karfin tuwo.

Sojoji sun kwace wasu kayayyaki na mayakan, wadanda su ka hada da bindigar harbo jirgin yaki da roka biyu da bindigogi samfurin AK 47 biyu da alburusan bindiga mai sarrafa kan ta guda 15 da kuma alburusan bindiga mai carbi 15.