Home Labaru Kasuwanci Nijeriya Za Ta Fara Saida Wa India Danyen Man Fetur – NNPC

Nijeriya Za Ta Fara Saida Wa India Danyen Man Fetur – NNPC

520
0
Kamfanin NNPC
Kamfanin NNPC

Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPC, ya ce zai fara saida wa kasar India kashi 10 cikin 100 na danyen mai domin taimaka wa kasar warware matsalar makamashi da ta ke fama da ita.

Kasar India, wadda ita ce kasa mafi yawan al’umma ta biyu a duniya, tana bukatar man fetur daga wasu kasashe domin warware matsalar makamashi da ta ke fama da ita a halin yanzu.

Shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari, ya ce Nijeriya za ta cigaba da tallafa wa kasar India wajen warware matsalar makamashin da ta ke fama da ita ta kowace hanya.

Mai magana da yawun hukumar Ndu Ughamadu, ya ce Mele Kyari ya bayyana haka ne, yayin da wakilin kasar Indiya Abhay Thakur ya kai ziyara helkwatan hukumar da ke Abuja. Mele Kyari, ya ce yarjejeniyar fahimatar juna da Nijeriya da kasar India su ka rattaba hannu a kai za ta karfafa dangantaka a tsakanin kasashen biyu.