Home Labaru Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Yi Wa Dattawan Arewa Raddi

Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Yi Wa Dattawan Arewa Raddi

275
0
Oluwarotimi Akeredolu, Gwamnan Jihar Odo
Oluwarotimi Akeredolu, Gwamnan Jihar Odo

Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Nijeriya, sun maida martani a kan jawabin da aka alakanta da kungiyar Dattawan Arewa, inda su ka bukaci Fulani mazauna yankin kudancin Nijeriya su dawo arewa.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Odo Oluwarotimi Akeredolu, ya ce ba tare da kudirin musayar yawu da wani ba, wajibi ne a matsayin su na wakilan al’ummar yankin kudu maso yammacin Nijeriya su yi watsi da wannan furuci da ka iya haddasa rabuwar kawuna da koma-baya.

Ya ce gwamnoi da mutanen kudu maso yamma su na aiki tukuru a kan kalubalen tsaro da ake ciki yanzu, tare da kudirin neman mafita domin magance abubuwan da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Kungiyar ta kuma jadadda jajicewar gwamnonin da mutanen yankin wajen ganin hadin kan kasa, yayin da su ke ci-gaba da magance kalubalen.

A karshe ta yi kira ga dukkan Fulani da ‘yan Nijeriya daga sauran yankuna da kuma mazauna yankin kudu maso yamma su yi watsi da kiran da kungiyar dattawa arewa ta yi da ma na sauran kungiyoyi marasa amfani.