Home Labaru Tsarin Aiki: Sojojin Nijeriya Sun Nesanta Kan Su Daga Bidiyon Cin Zarafi

Tsarin Aiki: Sojojin Nijeriya Sun Nesanta Kan Su Daga Bidiyon Cin Zarafi

456
0

Rundunar sojin Nijeriya ta nesanta kan ta daga wani bidiyo da ya bulla a yanar gizo, wanda ke nuna wasu sojoji su na azabtarwa tare da kisan wani da ake zargin dan Boko Haram ne.

A cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, rundunar ta ce ka’idojin aiki sun haramta wa dakarun ta cin zarafin mutane, don haka bidiyon abin Allah-wadai ne.

A karshen makon da ya gabata ne, aka ga wasu sojoji a cikin bidiyon sun harbe wani da aka ce dan Boko Haram ne, bayan sun ja shi a kasa hannayen sa daure da igiya sannan su ka cilla shi cikin rami su ka kuma harbe shi.

Rundunar ta ce tuni ta kaddamar da bincike game da bidiyon da nufin gano wadanda su ka aikata hakan, kuma za a sanar da jama’a sakamakon binciken.

An dai gargadi dakaru game da cin zarafin wadanda ake zargi, duk kuwa da irin yadda ake bukatar samun bayanai daga gare su ko kuma girman abin da su ka aikata.

Leave a Reply