Home Labaru Kwanan Nan Shinkafa Za Ta Yi Arha Takyaf – Bagudu

Kwanan Nan Shinkafa Za Ta Yi Arha Takyaf – Bagudu

297
0
Atiku Bagudu, Shugaban Gwamnonin, APC
Atiku Bagudu, Shugaban Gwamnonin, APC

Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya ce albarkar da aka samu a fannin noman shinkafa a wannan daminar zai taimaka wajen karyar da farashin shinkafa ta yi arha takyaf.

Bagudu, wanda shi ne Shugaba Kwamitin Shugaban Kasa na Noman Shinkafa da Alkama, ya bayyana haka ne a garin Argungu, yayin da ake gudanar da taron ganawa da manoman shinkafa na yankin.

Ya ce Albarkar noman da aka samu a wannan daminar zai rage tsadar shinkafar da ake nomawa a nan gida, kuma hakan zai kara rage bukatar shigo da ta fasa-kwauri, sannan ta nan gida za ta yi arhar, ta yadda duk irin talaucin mutum ba zai kasa sayen ta ba.

Bagudu ya kuma shaida wa manonan cewa, nan ba da dadewa ba gwamnatin sa za ta shigo da kananan injinan casar shinkafa ta raba wa manoma, domin karfafa ingancin shinkafar da manoman ke cashewa su na kaiwa kasuwanni.