Home Labaru Yaki Da Rashawa: Kungiyar Kasashen Afirka Ta Karrama Ibrahim Magu

Yaki Da Rashawa: Kungiyar Kasashen Afirka Ta Karrama Ibrahim Magu

277
0
Ibrahim Magu, Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, EFCC
Ibrahim Magu, Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, EFCC

Cibiyar yaki da rashawa ta kungiyar kasashen Afirka, ta karrama shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu a matsayin gwarzon yaki da rashawa a nahiyar Afirka baki daya.

Kungiyar ta sanar da karrama Magu da lambar yabo ta ‘Jagoran yaki da rashawa na musaman a Afirka’ ne a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Wakilin Nijeriya a majalisar Dakta Tunji John Asaolu ya bayyana haka, inda ya ce za a karrama Magu ne saboda kwazo, da kwarewa da kuma kokarin da ya ke nunawa wajen yaki da rasahwa a Nijeriya.

Ya ce su na sa ran karramawar za ta karfafa yaki da rashawar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi a Nijeriya.  

Mista Tunji ya ce, za a gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na Ladi Kwai da ke Otal din Sheraton a birnin tarayya Abuja, da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019.