Home Labaru Nemi Buhari Ya Shiga Tsakanina Da EFCC – Rochas Okorocha

Nemi Buhari Ya Shiga Tsakanina Da EFCC – Rochas Okorocha

46
0

Tsohon gwamnan Jihar Imo Sanata Rochas Okorocha, ya bukaci Shugaba Buhari ya shiga tsakanin shi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC.

Okorocha ya bayyana haka ne, jim bayan ganawar sa da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja, inda ya ce ya gabatar wa shugaba Buhari koken cewa EFCC ta daina yawan muzanta shi da neman harzuka shi a kan shari’ar zargin almundahanar naira biliyan 2 da miliyan 900.

Ya ce ya nemi Shugaba Buhari a matsayin sa na mai mutunta doka da son kiyaye ka’ida, ya sa baki a kan lamarin sa da hukumar EFCC don ta bi umarnin kotu.

Rochas ya kara da cewa, ya na da hukunci da umarnin kotu biyu, da hukunce-hukunce har uku a wurare daban-daban, wadanda su ka hana EFCC cin zarafi da kuma harzuka shi, amma hukumar  ta ki bin doka.

Sana Okorocha, ya ce ya kuma nemi hukumar EFCC ta daina azarbabi a kan bin duk wani abin da ya shafe shi.