Home Labaru Kungiyar ASUU Ta Yanke Kauna Da Gwamnatin Tarayya

Kungiyar ASUU Ta Yanke Kauna Da Gwamnatin Tarayya

46
0

Kungiyar malama jami’a ta Nijeriya ASUU, ta nuna shakku game da cika alkawurran da gwamnatin tarayya ta dauka na samar da mafita ga matsalolin da fannin ilimin Nijeriya ke ciki.

Haka kuma, Kungiyar ta ce za ta fara yajin aikin sai baba ta gani nan ba da jimawa ba.

Kungiyar, ta kuma bayyana abin da ke faruwa a halin yazu a matsayin abin kunya, musamman yadda gwamnati ke ci-gaba da kare tsarin biyan kudi na IPPIS, duk da zargin cewa akwai almundahana a cikin sa, kamar yadda ya ke a cikin rahoton da babban akanta na kasa ya gabatar a gaban Majalisar dattawa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ASUU ta nuna fushin ta a kan yadda aka rika zaman sasanci tsakanin ta da gwamnati, game da yadda za a farfado da ilimi sai dai gwamnati ta gaza dabbaka abin da ta ke ikirari a baya.