Home Labaru Dalilin Da Ya Sa Na Fice Daga PDP Na Koma APC –...

Dalilin Da Ya Sa Na Fice Daga PDP Na Koma APC – Sanata Bwacha

68
0

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa Sanata Emmanuel Bwacha, ya bayyana dalilan da su ka sa ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Emmanuel Bwacha daga jihar Taraba, ya ce mutanen jihar sa da mazabar sa ne su ka ba shi shawara, ganin yadda jam’iyyar APC ta yi manyan ayyukan da PDP ba ta yi ba a jihar.

Ya ce akwai ayyukan da gwamnatin Buhari ta aiwatar, wadanda jihar ba ta taɓa ganin irin su ba, don haka ya ga ba ya da abin zai saka wa shugaba Buhari illa ya koma jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar APC na riƙon ƙwarya Mala Buni, ya yi wa Bwacha iso zuwa fadar shugaban ƙasa domin a yi ma shi wankan shiga jam’iyyar APC.

Bisa ga tsarin dokar Nijeriya dai, duk sanata ko dan majalisar wakilan da ya sauya sheka daga wata Jam’iyya zuwa wata zai sauka daga mukamin da ya ke a kai da kujerar sa a zauren majalisa.